Labaran Duniya

Qalu’innalillahi Rabon Ajali: Yadda Matashi Ya Nutse a Rijiya Wajen Ciro Bokiti…

Rabon Ajali: Matashi Ya Nutse a Rijiya Wajen Ciro Bokiti.


Rabon Ajali: Matashi Ya Nutse a Rijiya Wajen Ciro Bokiti
Sharif Addubawi by Sharif Addubawi February 20, 2023 Reading Time: 2 mins read
Rabon Ajali: Matashi Ya Nutse a Rijiya Wajen Ciro Bokiti


Wani matashi mai shekara 27 a duniya ya nutse a rijiya yayin ƙokarin ciro bokitin da ya faɗa cikin rijiya.

Lamarin dai ya auku ne a ƙauyen Alaja cikin ƙaramar hukumar Akinyele ta jihar Oyo. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

KU KARANTA KUMA: Sauya Fasalin Naira: Gwamnonin APC 3 Sun Gana Da Ministan Shari’a

A cewar majiyar, mamacin yaron mota ne sannan da shi da ogan sa direban babbar mota suna kan hanyar su ta zuwa wani waje ne a jihar a ranar Asabar, 18 ga watan Fabrairun 2023.

Kawai suna tsaka da tafiya sai motar ta lalace musu a kusa da ƙarshen mahaɗar Powerline/Moniya na sabuwar hanyar Ibadan zuwa Oyo.

An samo cewa direban ya ajiye motar a gefe guda yayin da mamacim ya ɗauki bokiti ya tafi neman ruwan da za a sanyawa lagireton motar. Ya garzaya wajen shagunan dake a ƙauyen na Alaja inda ya ci karo da rijiyar.

Wani shaidar ganau ba jiyau ba, ya bayyana cewa bayan mamacin yaje wajen rijiyar, sai ya nemi igiya bai samu guga ba. Daga nan sai ya ɗaura igiya a jikin bokitin ya sanya cikin rijiyar.

Kawai sai igiyar ta tsinke bokitin ya tsunduma cikin rijiyar. Kawai sai yaron motar ya shiga cikin rijiyar inda ya nutse.

Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa sun fahimci yaron motar ya nutse ne cikin rijiyar bayan da direban motar ya hango takalmansa a gefen rijiyar..

Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button