Labaran Duniya

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un; An Kama Wasu Muggan Makamai A Motoci 2 Zasu Kai Katsina Daga Jiahr Lagos.

Kalli Makaman Da Aka Kwato Bayan Yan Sanda Sun Kama Motoci Biyu Da Suke Tafiya Daga Lagos Zuwa Katsina

Wasu motocin bas guda biyu da ke jigilar kaya masu yawa daga Legas zuwa jihar Katsina sun shiga hannun jami’an ‘yan sandan Najeriya.

Jami’an rundunar ‘yan sandan yankin Ikorodu ne suka tare motar a unguwar Poromope Estate, kan titin Ijede a Ikorodu a jihar Legas.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Asabar, 24 ga watan Satumba, 2022, an kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a akan wadannan muggan alburusai da makamai.

Wadanda ake zargin sun hada da Tukur Abdullah ‘m’ mai shekaru 35, Muazu Telim ‘m’ mai shekaru 50, da Dahiru Idris ‘m’ mai shekaru 36.

Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka Digitalskil.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button