Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un, Jama’a Ku Taya Ni Da Addu’a, Ina Cikin Matsanancin Hali Nayi Wata Rashin Lafiya

Digitalskil.com ta ruwaito daga majiya mai karfe cewa Tsohon ɗan wasan kwaikwayon nan Alhaji Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura).
Ya bayyana cewa ya na buƙatar addu’a daga al’ummar Annabi saboda yanayin rashin lafiyar da ya ke ciki, wanda ya kai har an kwantar da shi tsawon lokaci a wani asibiti a Kano.
Bankaura, wanda a yanzu ake kira Yakubu Ka-Fi-Gwamna saboda rol ɗin sa a diramar ‘Kwana Casa’in’ ta gidan talbijin na Arewa24.
Ya na daga cikin daɗaɗɗun ‘yan wasan kwaikwayo da Arewa ke ji da su, domin ya fara dirama ne tun kafin a assasa masana’antar shirya finafinai ta Kannywood.
Lokacin da wakilin mujallar Fim ya samu labarin rashin lafiyar, ya garzaya gidan sa da ke unguwar Hotoro Tsamiyar Boka a ranar Litinin, 19 ga Satumba, 2022
Daga can aka tura shi wani asibitin kuɗi mai suna Pinnacle Special Hospital da ke unguwar Hausawa kusa da Masallacin Murtala inda ya same shi a kwance magashiyan.
Wakilin mu ya ruwaito cewa da ƙyar ya gane ɗan wasan saboda yadda rashin lafiyar ya ci ƙarfin sa, ya zama kamar ba shi ba.
Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka Digitalskil.com