Innalillahi Wainna Ilaihi Rajiun: An Kama Wani Matashi da Kan Gawar Wata Mata A Makabartan Musulmi

Subhanallah! Digitalskil yau na tafe da wani labari ne mai ban takaici akan yadda Wani matashi dan shekara 28, Ismail Adewuyi,
An kama shi ne da kan wata mace a makabartar musulmi da ke Osun.
An kama wani matashi dan shekara 28 mai suna Ismail Adewuyi ne a ranar Asabar dinnan da da gabata da kan matar ne a wata makabarta da ake zargin ya hake ramin ta ne kana ya yanke kan nata domin yin tsafi da shi.
Wani dan kungiyar mafarautan Najeriya Isa Usman ne ya kama wanda ake zargin a Ede.
Adewuyi, kamar yadda binciken ya nuna, an kama shi ne da misalin karfe 1 na daren ranar Asabar a makabartar musulmi, Oke Yidi Abere, a titin Ede.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola, ya shaidawa DAILY POST cewa da misalin karfe 1:25 na daren ranar Asabar,
Usman dan Najeriya mafarauci a Ede ya kama wani Ismail Adewuyi na Oke-Ola, unguwar Agbagudu a Ede, a kusa da makaabartan dauke da wani buhu.
Ko da suka yi arba sai ya fahimci kamar ba shi da gaskiya, nan take kuwa ya nemi da ya san menene a cikin wannan buhu.
Bayan turjiya da ya fuskanta, a karshe dai ya tankwarashi da karfin tuwo inda ya kwace buhun, kwatsam sai ga kan wata mata a cikin sabuwar gawa ce, bai yi watawata ba sai ya mika ahi ga hukuma.
To amma dai a cewar kakakin dan sandan, ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kuma hakika za a dauki dukkan matakin hukuncin da ya kamata idan aka same shi da laifi.
Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka Digitalskil.com