Labaran Duniya

Innalillahi; Yadda Garkuwa Da Mutane Sukayi Gaba Da Wasu Matan Aure Biyu A Hanyar Sokoto..

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un Yanzu Yanzu Muke Samun Wani labari Mara Dadi Akan Cewa Masu Garkuwa Da Mutane Sunyi Garkuwa Da Wasu Yan Mata.

Wasu mutane matafiya yan mata sun shiga hannun masu garkuwa da mutane daga hanyar sokoto zuwa jihar katsina dake nigeria domin kaiwa wata ziyara ta musamman.

Masu garkuwa da mutane sunyi gaba da wasu fasinjojin motar jihar sokoto zuwa garin kano da misalin karfe 1:00 na daren jiya wayewar yau alhamis a unguwar more dake karamar hukumar kware ta jihar sokoto.

Cikin matan da suka tafi dasu akwai wata baiwar allah mai suna maryam ahmad wacce ta kasance matar aure ce yayin da’ a wannan lokacin suka bata umarnin data ajiye jaririn da take tare dashi kafin su, tafi da ita.

Yanzu haka dai wannan lamari yana matukar baiwa mutane mamaki yayin da jama’ar gari sukayi allah wadai har takai ga sunkai koken su, wurin jami’an tsaro domin nuna goyon bayan su akan kubutar da matan.

Jami’an tsaron ‘yan sandan jihar ta sokoto sun bayyana cewa zasu ceto matan daga hannun masu garkuwa da mutanan nan bada jimawa ba, a cewar jami’an yan sandan jihar ta sokoto.


Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka Digitalskil.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button