Yadda Wani Matashi Ya Rasa Ransa Yayi Ceto Saniyar Sa A Kogi Kalli Video…

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Duk Wani Mutum Mai Imani Indai Ya karan ta wannan labarin sai yayi kuka da idon sa kamar yadda a yanzu haka ga Cikakken Bayani ka kalla.
Matashi Mai suna Adamu Musa dan kimanin shekaru 18 da yake zaune a unguwar magina a Cikin garin Buji a jihar Jigawa ya rasa ransa a dai dai lokacin da yake kokarin ceto saniyar sa data zame ta wada kogi.
Kakakin Jami’in hulda da jama’a na rundunar farar hula ta, NSCDC, reshen jihar Jigawa CSC Adamu Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a 4 ga watan Satumba.
Ya ce lamarin ya faru ne a jiya Asabar, da misalin karfe 02:00 na rana, lokacin da matashin ya kaɗa shanunsa guda biyu zuwa gona, ya kuma bar su su yi kiwo a kusa.
Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka Digitalskil.com