Labaran Duniya

Innalillahi; Daga Karshe Kalli Bidiyon Yadda Zama Kotu Ya Kasance Tsakanin Fatima Wacce Aka Yankewa Kafa..

Innalillahi Wa’inna Ilaihi raji’un Yanzu yanzu a shiga Zaman Kotu domin a yanzu haka za a biwa wacce Wani Matashi yayi Sanadiyar Yanke mata kafa.

An shiga kotu a yau Litinin domin sauraren shari’ar fatima wacce aka yankewa kafa sakamakon buge ta da mota.

Saidai kamar yadda amihad.com ta samu labari ‘yan uwan Fatima sun soma zargin ba za a yi musu adalci ba saboda yaron dan masu hali ne.

A yau ne aka shiga kotu wajen zaman yanke hukunci ga wanda ya yi sanadiyar buge Fatima da mota, amma Alkalin kotun bai samu zuwa zaman na yau ba, saidai kuma an samu hargitsi wanda ya yi sanadiyar jami’an tsaro suka hana ‘yan jarida da sauran al’umma daukar hoto ko bidiyo a wurin.

A dalilin hakan ne wasu a bangaren Fatima suna zargin kotun da ba za ta iya musu adalci akan wanda ya yi sanadiyar buge `yar su ba saboda bangaren iyayen yaron masu kuɗi ne sannan kamar dai ana so a canza labarin.


Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka Digitalskil.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button